Thursday, 26 January 2017

Masu Hikima : Masu Hikima : Masu Hikima : Masu Hikima : MANUFAR ...

SURATUL MA'IDAH: SU WANENE ALKAFIRUN, AZ-ZALIMUN, ALFASIQUN?

Acikin Suratul Ma'idah Ayata 44 Da Ta 45 Dakuma Ta 47, Allah S.W.T Yakira Nau'in Wasu Mutane Da Kafirai, Azzalumai Dakuma Fasiqai Dukkansu Akan Kin Aiki Da Abinda Yasaukar Musu Na Hukunci. Sai Dai Malamai Masana Tafsiri Kuma Magabata SunYi Bayani Akan Tayaya Mutum Zai Zamo Kafiri Ko Azzalumi Kokuma Fasiqi Abisa Hukunce-hukuncenda Ya Saukarwa Bayinsa. Ga Bayaninsu Kamar Haka:-
1. ALKAFIRUN: Duk Wanda Yayi Hukunci Da Dokar Da Bata Allah Ba Yana Ganin Yahalatta, Ayi Wannan Hukuncin Bada Abinda Allah Ya Saukarba. To Shine Allah Ke Nufi A Ayata 44
2. AZ-ZALIMUN: Wanda Yayi Aiki Da Dokar Da Bata Allah Ba,amma Yasan Wannan Abinda Yayi Sabone To Shine Azzalumi, Kamar Yadda Ya Bayyana Ayata 45.
3. ALFASIQUN: Kamar Yadda Yazo A Ayata 47 Acikin Suratul Ma'ida Da Fadin Allah Alfasiqun, To Anan Ana Nufin Wanda Yayi Aiki Da Dokarda Bata Allah Ba, Ta Hanyar Amsar Rashawa To Shine Fasiqi.
Allah Ne Mafi Sani!

No comments:

Post a Comment