Monday, 27 February 2017

MUTUM BAKWAI

MUTUM BAKWAI SUNA CIKIN INUWAR ALLAH,
ARANAR DA BABU WATA INUWA SAI TASA:
1. Shugaba mai adalci.
2. Da Matashi wanda ya rayu cikin bautar Allah.
3. Da mutumin da koyaushe zuciyarsa take
ta'allake da Masallaci.
4. Da Mutum biyu wadanda sukayi soyayyar Juna
domin Allah. Suka hadu akan haka, kuma suka
rabu akan haka.
5. Da Mutumin da wata Mace Kyakyawa,
ma'abociyar Matsayi ta kirashi Izuwa Fasikanci,
amma (bai bata hadin kai ba) yace NI INA JIN
TSORON ALLAH.
6. Da Mutumin da zaiyi sadaka ya boyeta, har sai
da hannunsa na haggu bai san abinda hannunsa
na dama ya bayar ba.
7. Da Mutumin da ya tuna Allah, shi kadai a'boye,
Har idanunsa suka zubar da hawaye.
Muslim, hadisi na 1,031).
Allah Yasa Mudace

No comments:

Post a Comment