《KISTUL HINDI 》
Kistul Hindi nau'in Icce ne da labarawa da mutanen Sin da sauran Kasashen yankin Asia da Latin, ke amfani dashi acikin abinci da kuma wurin maganin cututtuka da dama.
Shi Kistul Hindi yana zuwa ne akasashenmu na yammacin Africa anau'I na gari dakuma mai (amma asalin icce kamar yadda zamuga hotonsa, a kasan wannan kasidar) amma inda ake sarrafashi zaka same shi anau'uka daban-daban. Shiyasa zanyi bayani akan Garinsa saboda shi muka fi sani tareda sauqin samunsa.
Shi GARIN KISTUL HINDI Yana magance cututtuka da dama kamar: Ciwon mara yayin al'ada, daidai ta haila, magance dafi na wuka ko na maciji da kunama, maganin kumburi ko rauni, maganin aljani, sihiri, karfin maza, tsutsar ciki, magance matsalolin ciki.dasauransu.
#YADDA AKE SARRAFASA:
1. DOMIN MAGANCE MATSALAR HAILA, CIWON MARA, TSUTSAR CIKI, SIHIRI, DA MATSALAR ALJANI (ISKA) SAI ADEBI COKALI 5 NA GARIN KISTUL HINDI SAI GARIN HABBATUSSAUDA COKALI 3 SAI MAN ZAITUN COKALI 7 SAI GARIN ZAITUN COKALI 3 SANNAN AGAURAYESU AZUBA ZUMA KOFI DAYA KARAMI AKARA CAKUDEWA. ANEMI WURI MAI MATSAKAICIN YANAYI A AJE ARIKA SHAN COKALI 3 SAU 3 ARANA. MAFI KARANCIN SHAN MAGANIN KWANA 3 ZUWA 7 GA MASU LARURAR AL'ADA KO MATSALAR ALJANI.
2. GA MASU SON KARIN KARFIN MAZA KUMA SU SAMU GARIN KISTUL HINDI SU HADA DA NONON RAKUMI KO ZUMA SU MOTSE SU RIKA SHA IDAN ZASU KWANTA. ANA KUMA ZUBA KIMANIN COKALI 1 ABAKI SAI ABI DA RUWA ASHANYE.
3. MATSALAR DAFI KUWA SHIMA ANA HADIYAR GARINNE DA RUWA KO AHADA DA ZUMA KO NONO NA SHANU ASHA. HAKAKUMA GA MAI RAUNI KO YANKEWA ZAI IYA SHANSA KAMAR YADDA MUKA AMBATA HAKAKUMA ANA TAFASA RUWAN ZAFI DA GARIN AWANKE INDA DAFIN YAKE KO GASAWA KOKUMA ANEMI MAN ZAITUN AKWABA DA GARIN ASHAFE GURIN.
DA IZININ ALLAH ZA'ASAMU FA'IDAR MAGANCE WADANNAN CUTUTTUKA DA AMFANI DA GARIN KISTUL HINDI.
Allah yasa mu dace.
No comments:
Post a Comment