RUQYAH!!!
Micece Ruqyah?
Ruqyah na nufin yin wata addu'a ta hanyar furta wasu lafuzza wadanda suka zo, anassin Ayoyin Alkur'ani ko sukazo daga bakin manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agaresua), domin karantawa da tofawa, mai fama da wata cuta, cutar ta shafi fatane ko zuciya kokuma gabbai ta hanyar neman waraka daga Allah ta'ala shi kadai.
Atakaice: ita Ruqyah addu'ah ce da mutum zaiyiwa kansa ko wani dan'uwansa.
-------------------------------------
Allah ta'ala yana fada acikin Suratul baqara cewa: "WALLAHI ZAMU JARABCEKU DA WANI ABU DAGA TSORO DA YUNWA DA NAKASA DAGA DUKIYA DA RAYUKA DA YAYAN ITACE,KUMA KAYI BUSHARA GA MASU HAKURI........"
Donhaka, ita jarabawa cikin rayuwar mutum mai kyau da mara kyau duk Allah ne yake kaddaroma kowa. Yawanci mutane kanyi kuskure suce ai mutanen kwarai sune ke ba'a jarabawa, toh amma abin ba haka yake ba, hasalima sune sukafi jarabtuwa, domin Annabi SAW yana fada cewa: "wadanda akafi jarabta sune Annabawa sai mutanen kirki,sai kuma kowa gwargwadon imaninsa" ibn majah ya ruwaitoh sa.
Idan Allah yana jarabtaka to alamace ta soyayyar Allah akanka,domin kankarema zunubi akeyi. Hakika akwai jarabawa cikin alkhairi ko sharri.
-------------------------
Karin bayani: Mu na kara Isar da wasiyyar mu, ga mai karanta wannan kasidar, akan ya kiyaye tare da yawaita Azkar(ambaton Allah). Shi ambaton Allah na samarwa bawa, nutsuwa da samu lafiya dakuma biyan bukatu da yawaitar Arziki.
Sannan akwai wasu lokutta kebantattu da akeson bawa ya himmatu da yin Azkar.
Ya tabbata ahadissai mafi dacewar lokaci shine lokacin da aka ruwaito manzon rahama kan yi azkar dinsa wato da safiya(bayan sallar Asuba) dakuma yamma(bayan sallar Asar) sannan da dare(lokacin kwanciya).
-------------------------------
ABUBUWANDA AKE KARANTA WA YAYIN RUQYAH:-
kafin mu jero ayoyi da surori na ruqyah yakamata mudanyi matashiya akan wadannan ababe kamar haka:
1. Sharuddan addu'o'i:
- Addu'ar ta kasance da ayoyin alkur'ani akayi kokuma wadanda shari'a tazo dasu ta bakin fiyayyen halitta SAW.
- Ta zamo da harshen larabci, idan da iko.
- Kudurce cewa wannan addu'ah bata tasiri sai da izinin ubangiji,kuma waraka daga gareshi take.
2. Sharuddan mai ruqyah: -
Mai maganin(ruqyah) yazamo musulmi, kuma yazamo mutumin kwarai mai tsoron Allah,kuma yinta alokacinda yafi tsoron Allah zatafi tasiri.
-zuciya da harshe su hadu aguri daya tahanyar fuskantar Allah ta'ala da gaskiya lokacin addu'ar. Kuma mutum yayiwa kansa shine yafi inganci saboda mutum shine yafi bukatuwar kansa bisa ga waninsa. Kamar yadda wanda yake cikin kunci da bukatauwa Allah yafi saurin karbar addu'arsa.
3. Sharuddan wanda ake yiwa ruqyah (addu'ah): -
Yazamo mutum ne mai imani da Allah,kuma na kwarai. Kuma gwargwadon imani gwargwadon tasirin addu'ar. Allah yana fada cewa: "MUNA SAUKAR DA WARAKA DAGA ALKUR'ANI,KUMA RAHAMACE GA MUMINAI,BA ABIN DA ZAI KARAWA AZZALUMAI FACE HASARA".
-Fuskantar Allah da gaskiya,wurin fatan Allah ya bashi lfy.
-kada yayi gaggawar neman karbar addu'ar daga Allah. Saboda hadisin da bukhari da muslim suka fitar inda Annabin rahama SAW yakecewa: ANA KARBAR ADDU'AR DAYANKU MATUKAR BAIYI GAGGAWABA,YACE" NA ROKA BA'A KARBA MUN BA".
4. hanyoyin addu'ah:
1. Karanta addu'ar tareda yin tofi(wato tofa miyau inda keda larurar).
2. Hakama karanta addu'ar batareda tofiba.
3. Tofa yawu asaman dan yatsa atabo kasa sai ashafi gurin larurar.
4. Karanta addu'ar tareda shafa gurbin da yake ciwon.
5. Karanta addu'ar atofa cikin ruwa.
------------------------------
YAYA RUQYAH ZATA ZAMO?
Ya halatta ayi ruqyah da ayoyi da surori da kuma azkar dinda suka tabbata ga fiyayyen halitta, hakakuma haramunne ayi da ababenda suke musharaka ga Allah kamar nemawa marar lfy tsari da sunan wasu aljannu da kuma irin abinda ba'a fahimtar lafuzzan, domin kubuta daga wata alama ta shirka acikin hakan,saboda Annabi SAW yace acikin hadisin Muslim 10/167" Ba matsala don anyi magani(ruqyah wurin addu'ah) ga abinda baizamo shirka ba".
-----
SURORI MASU AMFANI WURIN RUQYAH DA SUKE WARAKA GA KOWACE CUTA TA JIKI KO TA ISKA:--
@SURATUL FATIHA: ankarbo hadisi daga Kharijah dan sult daga baffansa yace: nazo gun manzon Allah SAW nayi masa sallama sai ya amsamin,sai na riski wasu mutane suna tareda wani mutum mahaukaci,sai dangin wannan mutumin suka cemin munsamu labarin abokinka(ko abokinku) yazo da alkhairi,shin awurinka akwai wani abu da zaka yi wannan ya warke. Sai yayi masa Ruqyah(addu'ah) da Suratul fatiha,sai Allah ya bashi lfy. Sai suka bani akuya,sai nazo gun Annabi SAW na bashi labari sai yace min (awata ruwayar yace min) ka fadi wani abu banda wannan surah? Nace a'a,sai yace min hakika kaci daga ruqyah ta gaskiyah" wato kayi magani da abinda shine mafi dacewa da inganci). Abu-dawud(hadisi mai lamba:3420) da Nisa'i(1032). Albani ya inganta hadisin.
@SURATUL BAQARAH( annabi SAW yana cewa:KADA KA MAIDA GIDAJENKU MAKABARTA,DOMIN SHAIDANU BASA ZAMA GIDAN DA AKE KARANTA SURATUL-BAQARAH" muslim(6/67) da Tirmizi(5/157)
@SURATUL IKHLAS DA FALAQ DA NAS: daga Uqbatu dan Aamir(ra) yace: ina rike da linzamin abin hawan Annabi SAW awurin wani yaki,sai yacemin ya Uqbatu fadi! Sai na saurari annabi,sai ya kara cemin fadi ya uqbah!! Sai nayi shiru ina saurare,sai yakara fada har sau 3,sai na ce mezan fada ya rasulullah? Sai yace min kakaranta Qulhuwallahu ahada(har karshen surar ya karantamin) sannan falaq da nas har karshe,damuka karanta su har karshe sai Annabi yacemin: BABU WASU SURORI MASU TSARI KAMAR WADANNAN) nisa'i ya ruwaito sa (8/250) Albani ya inganta hadisin. -
@ALKUR'ANI DUKKANSA WARAKANE: duk wata surah wadda take dauke da ambaton wani alkawari na ubangiji ko cikasa ga bayi,ko ambaton wuta da aljannu da shaidanu kamar suratul Muminun,Yasin,Safat
,Dukhan,Jinn.Hashr,Zalzalah,Qari'ah,Kafiruun,dss duka ana karantasu wurin Ruqyah,musamman ga masu fama da iska,ko sihiri. -----
# AYOYI: - DAGA CIKIN AYOYINDA AKE KARANTAWA YAYIN RUQYAH DON WARAKA DAGA CUTUTTUKA NA SIHIRI,ISKA,DA LARURA WADDA AKA KASA GANE AINIHINTA KO MAGANINTA AKWAI:
-ayata ta 36 cikin suratul fusilat.
- ayatul kursiyyu(kamar yadda yazo akissar wannan mutumin maiyiwa Abu-hurairah sata da daddare.(bukhari 4/487) -ayoyi biyu na karshen Suratul baqarah,kamar yadda bukhari yafitar 6/323.
-ayoyi ukku na cikin suratul A'raf(ayata 54-56)
-aya cikin suratu ali-imran(ayata 18).
-ayoyi hudu nacikin suratul muminun(ayata 115-118)
-ayata ta 3 cikin suratul jinn.
-ayoyi 10 nacikin suratus safat(ayata 1-10).
-ayata 21-24 cikin suratul hashr.
-ayata 31-34 cikin suratul rahman. -ayoyi biyu nakarshen suratul qalmi(51-52) INSHA ALLAHU DUK WATA CUTA DA TA GAGARA MAGANI INDAI ANA KARANTA WADANNAN SURORI DA AYOYI ZA'A SAMU WARAKA,KAMAR IRINSU HIV,CANCER,HAUKA,ISKA, DADAI MAKAMANTANSU.
IBN QAYYIM(R) YACE: duk wanda Alkur'ani bai warkar dashiba to babu abinda zai warkaddashi,inkuma Alkur'ani bai isar masa ba to babu wata isuwa da zaisamu gun Allah. Yacigaba dacewa: watarana ina a makka sai ciwo ya sameni sai na nemi mai magani na rasa bansamu wani maganiba da zanyi amfani dashi,sai nazamo inayiwa kaina magani(ruqyah) da Suratul fatiha sai naga tasirinta mai ban mamaki,nazamo ina dibar zamzam sai nakaranta fatiha na sha,sai gashi na samu waraka cikakka,har na zamo ina baiwa mutane magani akan hakan,kuma ya amfanesu.
@# akwai wata tsohuwa da likitocin jamus suka kasa gane larurarta suka ce sai dai iayalan su hakura don bazata warkeba,sai iyalan suka daketa suka kaita asibitin madinah tayi jinya can ta rassu,dama babu mai jiyya,suka dawo gida suna jiran suji ankirasu akan rassuwarta,sukaji shiru sai suka kawo ziyara gareta sai suka sameta cikin koshin lfy takumayi kiba,abinya basu mamaki,sai ake fada musu zamzam ne abin shanta koda yaushe.
-----------@-----------------
Wasu daga lafuzzan Hadissai da Manzon Allah yake karantawa marassa lafiya(wato yake fada idan zaiyi ruqyah ga marar lfy) gasu kamar haka:
#----
1. AS'ALULLAHAL AZIMA RABBAL ARSHIL AZIMI AN YASH FIYAK(SAU 7).
2. U'IZUKA BI KALIMATILLAHI TAMMAH,MIN KULLI SHAIDANIN WA HAMMAH,WAMIN KULLI AINIL LAMMAH(SAU 3).
3. ALLAHUMMA RABBAN NAS AZHIBIL BA'ASA WASHFI ANTAS SHAFI'U LA SHIFA'A ILLA SHIFA'UKA SHIFA'AN LA YUGHADIRU SAQMA (SAU 3)
4. ALLAHUMMA AZHIB ANHU HARRAHA WA BARDAHA WA WASBAHA(SAU 7).
5. HASBIYALLAHU LA ILAHA ILLA HUWA ALAIHI TAWAKKALTU WA HUWA RABBUL AZIMI(SAU 7).
6. BISMILLAHI ARQIYKA MIN KULLI DA'IN YU'ZIKA,WAMIN KULLI NAFSIN AU AININ HASIDIN,ALLAHU YASHFIYKA,BISMILLAHI ARQIYKA(SAU 3).
7. BISMILLAH(SAU 3) A'UZU BILLAHI WA QUDRATIHI MIN SHARRI MA AJIDU WAHAZIR.
________
Wadannan sune daga cikin Ayoyin Alkur'ani dakuma Addu'o'in da su kazo acikin Hadissan Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) da ake karantarwa, domin Neman TAIMAKON akan wata larura da samu mutum ko neman tsari akan dukkan musibu.